Birnin Legas, ko kuma Birnin Ikko, shi ne babban birnin Jihar Legas da ke Najeriya. Legas yana daya daga cikin birane mafi girma da yawan jama'a a Afirka da ma duniya baki daya. Legas ne birni na biyu mafi girma a Afirka, kuma na bakwai a duniya. Kimanin mutum miliyan 15.3 (a shekara ta 2022) ke rayuwa a Legas. Garin Legas na da mutane kimanin 23.5 million a shekara ta 2018, wanda ya maida shi babban birni mafi girma a nahiyar Afirka. Legas ya kasance cibiyar kasuwanci a jihar Legas da Najeriya gaba daya. Legas tana daya daga cikin birane goma masu habbaka da sauri a duniyaBabban birnin yana matsayin na hudu a kawo kudin shiga (GDP) a Africakuma akwai daya daga cikin tashar jiragen ruwa mafi hada-hada Afirka.Birnin Legas cibiya ne na ilimi, gargajiya a sassan Afirka da ke kudancin sahara. Legas a da gida ne ga mutanen Awori, wani reshe ne na Yarbanci na yammacin Afirka. Amma yanzu ta zama birnin tashoshin jiragen ruwa wanda ya samo asali daga tsibirai dabam-dabam. Gwamnatin tarayya ke gudanar da harkokin wannan babban birni har izuwa shekarar 1967 lokacin da aka rarraba birnin zuwa kananan hukumomi 7 da muke da su a yau. da kuma karin birane 3 wanda ya sa kananan hukumomin suka koma 13 wanda suka samar da jihar Legas na yau. Har wa yau, an mai da Ikeja ta zamo babban birnin jihar a shekara ta 1976, sannan Abuja ta koma babban birnin tarayya a shekara ta 1991. Wuraren da ake kira birnin Legas watau "Lagos Metroplitan Area" sun hada da manyan biranen jihar guda 16 har da Ikeja. Wannan manyan birane sun mamaye kashi 37% na fadin kasar Legas, sannan tana dauke da fiye da kaso 86% na mutanen jihar Legas. Akwai rudani game da ainihin yawan mutane birnin Legas. A kidaya da akayi na shekara ta 2006 ya nuna cewa akwai adadin mutane miliyan 8 a birnin. Sai dai gwamnatin jihar ta nuna rashin amincewarta ga adadin kidayan inda ta daki nata adadin da kimanin mutane miliyan 16. A shekara ta 2015 wani kundi wanda gwamnati bata tantance shi ya sanya mutanen Legas har zuwa kusa da jihar Ogun kimanin mutum miliyan 21.
Developed by StudentB